PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-03-05 (xsd:date)
?:headline
  • Haɗa nau’ukan abinci, ganyayyaki da itatuwa baya maganin ciwon amosanin gaɓoɓi (tl)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani rubutu da ke yawo a Facebook a Najeriya ya bada shawarar maganin amsonin gaɓoɓi, aka kuma jero nau’ukan abinci na yau da kullum kamar inibi, lemon tsami, zuma, citta da tafarnuwa a matsayin masu warkarwa. Rubutun na haɗe da inda za’a latsa a shiga wani shafi da ya kira kansa da Africa’s No 1 herbal medicine shop, wanda ya ke ɗauke da rubutu akan makamanciyar da’awar. Amosanin gaɓoɓ i, wanda akafi kira da awoka, awuka da aromoleegun a harshen Yarabanci, cuta ce da ke jawo kumburi, raɗaɗi da ƙagewar gaɓoɓi. Ire- iren amosanin gaɓoɓin da aka fi sani sun haɗa da austiyoraitis da romotoyad. Austiyoraitis shi yana afkuwa ne saboda yawan shekaru, yayin da rumatoyad ya fi yawa ga mata, a kuma ƙasashen da suka cigaba, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce. Shin da gaske wannan haɗi na maganin amosanin gaɓoɓi? Magani na danganta da musabbabin ciwo John Onuminya, Farfesa a fannin kula da ƙashi na jami’ar Ambrose Alli da ke jihar Edo, kudancin Najeriya, ya shaidawa Africa Check cewa, babu hujja a kimiyance da ta tabbatar da ingancin da’awar da aka rubuta a Facebook . Sababin ciwon amosanin gaɓoɓi na da yawa, don haka zaiyi wuya a ce ga maganin cutar guda ɗaya, Farfesan ya ce. Babban abun da masu fama da ciwon suka fi kuka da shi, shi ne raɗadin ciwo, kuma babu wani abu daga cikin waɗannan kayan haɗi da zai maganin raɗaɗin. Hanyar da kawai wannan haɗi zai yi tasiri shine abun da ake cewa tasirin filasibo. Ma’ana lokacin da mara lafiya ya yarda cewa wannan abun zai rage masa raɗadin ciwo- duk da cewa a zahiri haɗin babu abun da yayi. Omuninya ya shawarci masu fama da ciwo da su je su ga likita. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url