PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-04-06 (xsd:date)
?:headline
  • Babu hujjar cewa abun shan da ake yi da ganyen zoɓo a Najeriya yana jawo zuɓewar juna biyu (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙo da aka yaɗa a Facebook na cewa abun shan da ake haɗa shi da ganyayyaki a Najeriya yana jawo zubewar juna biyu ga mace mai ɗauke da juna biyu. Idan kuna da juna biyu, dan Allah kar ku sha ZOBO. An samu tabbatattun rahotannin matan da su kayi ɓarin juna biyu bayan sun sha zoɓo, saƙon ya ce. Zoɓo ana samun sa daga busasshen furen itacen roselle. Itace roselle wanda a kimiyance ake kira hibiscus sabdariffa, ya na cikin itatuwan gidan malvaceae. Ya kamata a kiyayi shan sa yayin da ake ɗauke da juna biyu? Babu wata hujja a kimiyance Farfesa Cyril Chukwudi Dim , ƙwararren likita akan mata masu juna biyu da lalurar da ta shafi mata na jami’ar Najeriya ya ce bashi da masaniyar wannan da’awar. Mutum ba zai alaƙanta zuɓewar juna biyu ga wani abu ba don ya faru sau ɗaya, hakan zai wuce gona da iri kuma zai zama ya ɓata wannan abun, likitan ya ce. Wani ƙwararren likitan mata masu juna biyu da lalura mata Farfesa Micheal Aziken ya ce, zoɓo baya cikin abubuwan da aka san suna jawo zuɓewar juna biyu, saboda ba’ayi bincike akan sinadaran da ke cikin sa ba. Aziken wanda ya ƙwaren akan hanyoyin taimakawa mata wajen samun juna biyu ya ce, jama’a su jira har a samu hujjoji ƙwarara da suka tabbatar zoɓo zai jawo zubewar juna biyu kafin su alaƙanta zoɓo da zuɓewar juna biyu. Da’awar da ke cewa zoɓo na jawo zuɓewar juna biyu a ɗauke ta a matsayin da’awar da zata jawo rigima, har sai an samu hujjar da ta tabbatar da hakan a kimiyance. Babu wasu ‘rahotannin tabbatattu’ na matan da juna biyunsu ya zuɓe bayan sun sha zoɓo. (so)
?:reviewRating
rdf:type
?:url