PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2023-01-04 (xsd:date)
?:headline
  • Babban bankin Najeriya bai ƙara wa’adin cirar tsofaffin takardun kuɗi ba (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • A TAƘAICE : Majalisar dokokin Najeriya ta umarci babban bankin Najeriya da ya ƙara wa’adin daina amfani da tsofaffin kuɗi. Duk da da’awowin da ke yawo a kafafen sada zumunta, bankin bai bayyana ko zai ƙara wa’adin ba. Za’a daina karɓar tsofaffin kuɗin a ranar 31 ga watan Janairu 2023, kamar yadda aka faɗa tun farko. Ya shigo yanzu: An ƙara wa’adin amfani da tsofaffin kuɗaɗe zuwa watan Yuni, a cewar wani saƙon Facebook da aka wallafa ranar 29 ga watan Disemba 2022. A ranar 26 ga watan Oktoba , Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana shirin sake sauyin fasalin takardun kuɗin ƙasa na Naira N200, N500 da N1000. Ya ce za’a sauya fasalin ne don magance matsalolin da suka danganci hauhawar farashi, yin jabun kuɗi, matsalar tsaro da wasu matsalolin. Emefiele ya ce ƴan Najeriya na da har zuwa ranar 31 ga watan Janairu don sauya tsofaffin kuɗaɗen su zuwa sababbi. Saboda sauya fasalin da akayi CBN ta fito da sabon adadin kuɗin da za’a cira . Mafi yawan kuɗin da za’a cira zai kasance N100,000 a tsahon mako guda ga ɗaiɗaikun mutane, da N500, 000 ga kamfanoni a tsahon mako guda. Daga baya kuma CBN ta sake adadin, ta ce ɗaiɗaikun mutane zasu iya ɗaukar adadin kuɗi har N500,000 tsahon mako guda, inda kamfanoni zasu iya ɗaukar har Naira milyan 5. A watan Disemba 2022, majalisar dokoki ta buƙaci CBN da ta ƙara wa’adin amfani da tsohon kuɗi daga ranar 31 ga watan Janairu 2023 zuwa 30 ga watan Yuni. An maimaita da’awar da ke cewa an amince da ƙarin wa’adin a wasu saƙonnin da aka wallafa a Facebook. Amma hakan ne a hukumance? Mun bincika. CBN bata aiwatar da umarnin ƴan majalisar ba Gidajen jaridar Najeriya na al’ada sun ruwaito cewa majalisar dokoki ta bawa CBN umarnin da ta ƙara wa’adin fitar da kuɗaɗe, amma kuma basu fitar da rahoton ko CBN ɗin ta amince da hakan ba. A watan Nuwamba 2022 , CBN ta wallafa a shafinta na Tiwita cewa za’a cigaba da amfani da tsofaffin takardun kuɗi na Naira har zuwa ranar 31 ga watan Janairu 2023, basu fitar da sanarwar sun ƙara wa’adin ba. Ba’a tabbatar da gaskiyar saƙon na kafafen sada zumunta ba. (so)
?:reviewRating
rdf:type
?:url