PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-03-30 (xsd:date)
?:headline
  • Ƙasar Canada bata bada muhalli ƙyauta ga baƙin haure (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Ɗaukar ma'aikatan gwamnatin Canada na shekarar 2022, kanun wani saƙo da ke yawo a WhatsApp a Najeriya. An watsa saƙon a wasu shafukan kafar sada zumunta ta Facebook ma. Saƙon ya haɗa da link ga wanda ke buƙatar komawa zama ƙasar Canada. Sannan saƙon ya umarci masu so dasu kasance sun kai shekaru 16 zuwa sama, ya zamana kuma suna jin harshen turanci. Saƙon yayi iƙirarin gwamnatin Canada ce ke ɗaukar ma’aikatan, kuma shirin ya haɗa da kuɗaɗen tafiya, muhalli da kayan kiwon lafiya. Hakan gaskiya ne? Mun bincika. Da alama ɗamfarar yanar gizo ce Link ɗin na kai mutum wani shafi mara tsari , inda ake umartar waɗanda suka ziyarci shafin da su bada bayanin inda za’a same su. Rubutun da ke shafin yana cike da kurakuran da suka saɓawa ƙaidar rubutu, alamar cewa ba ƙwararru bane suka tsara shafin, waɗanda su ne ya kamata ace su ke isar da saƙon gwamnatin ƙasar. Duk da cewa manema labarai sun ruwaito cewa gwamnatin Canada na shirin karɓar baƙin haure har 431 ,645 a shekarar 2022 a matsayin mazauna ƙasar na dindindin , amma dai babu wata kafar sadarwar ƙasar da ta ruwaito cewa gwamnatin na shirin ɗaukar ma’aikata ƴan ƙasashen waje guda 450,000. Sahihin shafin tiwita mallakin ofishin jakadancin ƙasar da ke Najeriya bai bayyana bayanin ɗaukar ma’akata a ƙasar ba. A watan Satumbar 2021, gwamnatin Canada ta wallafa wani rubutu da ke gargaɗin baƙin haure da su kiyayi ƴan damfara, sun kuma bayyana yadda za’a iya gane shafukan ƴan damfara. Duk alamu sun nuna cewa wannan damfara ce aka shirya don samun damar ɗaukar bayanan jama’a. Ba shi kuma da alaƙa da gwamnatin ƙasar Canada ta kowacce hanya. Don samun hanyoyin gane ƴan damfara a yanar gizo, a karanta bayanin hanyoyin gane su da mu kayi a nan . (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url