PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-03-05 (xsd:date)
?:headline
  • Ɓawon bishiyar ɗorawa na maganin hawan jini (sw)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wan i rubutu a wani shafin Facebook mallakin yan Najeriya Solarababa herbs yayi iƙirarin cewa ɓawon bishiyar ɗorawa zai kashe hawan jini. Rubutun ya bayyana yadda za’a haɗa maganin. A tafasa maganin da ruwa. A sha adadin (5ml) kullum har tsahon makwanni biyu. Amma wannan zaiyi maganin hawan jini? Mun bincika. A je a ga likita don samun kulawar da ta dace Ɗorawa wadda aka fi sani da bishiyar kalwa, bishiya ce da ke da amfani da dama kuma ake samun ta a ƙasashen Afrika da dama. Cutar hawan jini ko hauhawar jini, cuta ce mai matsanani ga kiwon lafiya, cutar na sa jini ya hau. Tana kuma zama barazana ga lafiyar ƙoda da zuciya. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce yankin Afrika ne ke da mafi yawan masu fama da cutar a duniya- kashi 27% na daga cikin mutane biliyon 1.13 da ke fama da cutar. Mun tuntuɓi Jacob Awobusuyi, Farfesa a fannin kiwon lafiya na jami’ar jihar Lagos don ya tofa albarkacin bakinsa akan wannan rubutu na Facebook . Bani da masaniya ko wani bayani akan hakan, ya ce. Maganin hawan jini ya fi ƙarfin a ce asha magani kawai. Akwai abubuwa da dama da ake don a shawo kan cutar. Awobusuyi ya ce masu fama da cutar hawan jini su je su ga likita don a basu kulawar da ta dace. Hukumar kiyaye yaɗuwar cututtuka ta Amurka, ta ce ta hanyar zuwa duba jini akai akai ne kawai za’a gano idan mutum na ɗauke da cutar. Daga cikin hanyoyin da za’ a kiyaye kamuwa da cutar hawan jini sun haɗa da cin abinci mai lafiya, rage ƙiba, motsa jiki, rage shan barasa da samun isasshen bacci. Africa Check ta tantance da’awa makamanciyar wannan da ke cewa garin abokado na maganin hawan jini da wasu cututtuka. (so)
?:reviewRating
rdf:type
?:url