?:reviewBody
|
-
Ku karbi damar zama a ƙasar Amurka ku nemi izinin samun katin zama ɗan ƙasa a gasar girin kad, a cewar wani ɓangare na wani rubutu da aka rarraba a Facebook. Wasu mamallaka shafukan Facebook a Najeriya sun yaɗa irin wannan da’awar . Duk kuma suna cewa waɗanda suka ci gasar ta katin zama zasu samu izinin zaman dindindin a Amurka, su kuma samu damar yin aiki a Amurkan. A kowacce shekara, Amurka na bada katin zama guda 55,000 ta hanyar shiga gasar, cewar ɗaya daga cikin rubutun . Katin zama wanda akafi sani da izinin zama na dindindin, shine abun da ke bawa waɗanda ba ƴan asalin ƙasar ba izinin zama na dindindin da kuma yin aiki a ƙasar. Amma shin waɗannan rubuce-rubuce akan yadda ƴan Najeriya zasu samu katin zama gaskiya ne? Mun bincika. An rufe neman izinin shiga gasar shekarar 2022 tun shekarar 2020 Rubutun na miƙa mutane ga wani shafin wanda shi kuma ya na cewa su rarraba link na shafin da abokansu guda 15 a WhatsApp ko a grup 5 na WhatsApp. Wannan misali ne na hanyar da ƴan damfara a Facebook ke amfani da ita wajen kara yawan jama’a a shafukansu. A lokuta da dama wannan ne alamar da ke nuna cewa tallan na ƙarya ne. Link ɗin neman aikin an saka shi a sahun wata hanya da ake amfani da ita don samun bayanan sirri kamar faswod da bayanan katin ku na banki, ta hanyar nuna cewa shafin abin amincewa ne. Da muka binciki yanar gizo akan2022 US lottery programme ya kai mu bureau of consular affairs , wanda sashe ne na jihar Amurka Lokacin rigistar shiga gasar samun takardar izinin shiga ta 2022 shine tsakanin 7 ga watan Octoba zuwa 10 ga watan Nuwamba 2020. Gasar ba’a buɗe ta ga ƴan Najeriya ba Bugu da ƙari, ƴan Najeriya basa cikin jerin rukunin da zasu iya shiga gasar ta shekarar 2022, kamar yadda dokar shiga gasar take a hukumance. Saboda an ƙirƙiri shirin ne don ya samar da dama ga masu son suyi ƙaura zuwa Amurka, waɗanda suka fito daga ƙasashen da ba’a cika samun masu shiga Amurka daga ƙasashen ba. Najeriya na cikin rukunin da ke yawan shiga Amurka. Waɗannan sune ƙasashen da sama da mutane 50,000 suka yi ƙaura zuwa Amurka a shekaru biyar ta dalilin iyalin su ko karatu. A kiyayi shafuka na bogi A watan Yuni na shekarar 2021, ofishin jakadanchi Amurka da ke Najeriya ya gargaɗi jama’a masu neman izinin komawa Amurka da zama, da su kiyaye da shafukan yanar gizo na ƙarya. Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya na sane da shafuka da saƙonni da ake ta yaɗawa da ke tallan gasar samun izinin zama a Amurkam. Duka waɗannan na ƘARYA ne! Saƙon na Twita ya ce. Sun kuma sanar da hanya mafi sauƙi wajen gane irin waɗannan shafuka na bogi: Adireshin dake da .gov ne kawai sahihiyar hanyar samun labaran da suka danganci bizar na gaskiya.
(sw)
|