PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-08-26 (xsd:date)
?:headline
  • Shugaban ƙasar Ghana Akufo-Addo bai cewa ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya Tinubu ya ajiye takara ya bawa abokin hamayyarsa Obi ‘dama’ ba (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya shigo harkokin siyasar Najeriya bayan ya bawa ɗan takara Bola Tinubu shawarar bawa abokin hamayyarsa Peter Obi hanya . A cewar wasu saƙonni da ke yawo a Facebook tun ƙarshen watan Yunin 2022. A bawa Peter Obi dama, ka tafi ka nemi lafiyar ka- shugaban ƙasar Ghana ya rubutawa Tinubu, wani nau’i na saƙon ke cewa. Za’a iya ganin wasu nau’ikan saƙon a nan , nan , nan da kuma nan . Za’a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a Najeriya a ranar 25 ga watan Fabrairu 2023. Tinubu , mai shekaru 70, shine ɗan takara daga jam’iyyar All Progressive Congress, yayin da Obi , mai shekaru 61, yana takara daga jam’iyyar Labour . Ƙasar Ghana ta na yammacin Africa. Shin shugaban ƙasarta ya rubutawa Tinubu cewar ya bawa Obi dama shi kuma ya je don neman magani? Mun bincika. ‘Gaba ɗaya ƙarya ce da kuma ɓarna’ Saƙon bai bayyana cikakken bayanin lokacin da Akufo-Addo ya rubutawa Tinubu wasiƙar ba. Babu kuma rahoton wata wasiƙa daga sahihan kafafen yaɗa labarai na gida da na waje, wanda tilas a samu hakan idan da ace da gaske anyi rubutun. A ranar 9 ga watan Agusta, Akufo-Addo ya wallafa wani saƙon hoton allon waya na wasu saƙonni a sahihin shafinsa na Tiwita, aka kuma saka tambarin cewa BOGI NE. A jerin saƙonnin Tiwita guda uku, ya bayyana da’awar a matsayin mai tayar da hankali , sannan kuma gaba ɗayanta ƙarya ce da kuma ɓarna , wacce babu alamun gaskiya a tattare da ita. Ban rubuta wata wasiƙa ga jigon APC ba, ba ni kuma da shirin yi. Ghana da Najeriya na da kyakkyawar alaƙa ta shekaru, ba kuma zai zama ni ne zan shiga al’amuran cikin gida ko na siyasar Najeriyar ba, Akufo-Addo ya rubuta , (so)
?:reviewRating
rdf:type
?:url