PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-07-27 (xsd:date)
?:headline
  • Masanin ƙwayoyin cuta Montagnier bai ce ‘ duk waɗanda aka yiwa allurar rigakafi zasu mutu cikin shekaru biyu’ (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Shin Luc Montagnier , ƙwararre akan ƙwayoyin cuta ɗan ƙasar Faransa yace duk waɗanda aka yiwa allurar rigakafi zasu mutu cikin shekaru biyu? Wannan rubutu ne da ke ta yawo a WhatsApp , Facebook da Instagram a Najeriya a watan Mayu 2021. Da dama daga rubutun da ake yaɗawa na nuna hoton Montagnier da taken : Duk waɗanda aka yiwa allurar rigakifi zasu mutu cikin shekaru biyu. Luc Montagnier wanda ya samu lambar yabo ta Nobel ya tabbatar da cewa babu dama mutum ya cigaba da rayuwa bayan ya yi kowacce daga alluran rigakafin, rubutu da ake fi yaɗawa ke cewa. A wata ganawa da akayi da shi, babban ƙwararre akan ƙwayoyin cuta ya ce: ‘ babu dama, sannan babu magani ga waɗanda suka riga sukayi allurar rigakafin. Mu shirya ƙona gawawwaki.’ Masanin kimiyar ya kuma goyi da bayan da’awowin wasu masana ƙwayoyin cuta bayan yayi nazarin abubuwa da ke ɗauke acikin alluran rigakafin. Duk zasu mutu daga haɓakar ƙwayoyin kare ƙwayar cuta a jiki. Babu abun da za a kuma cewa. Da dama daga rubutukan da ake yaɗawa an alaƙanta su ga wani rubutu a shafin yanar gizo na LifeSiteNews , wanda ke da taƙen: Wanda ya ci lambar yabo ta nobel: Taron llurar rigakafin Covid ‘kuskure ne da ba a amince da shi ba. Da gaske Montagnier ya ce duk waɗanda aka yiwa alllurar rigakafi zasu mutu cikin shekaru biyu? Ƙarya aka alaƙanta masa, ‘ labaran ƙarya aka kwaikwaya’ Wanda aka haifa a ranar 18 ga watan Agusta 1932, Luc Montagnier masanin binciken kimiyyyar ɗan asalin ƙasar Faransa, wanda ya samu tarin nasarori da suka haɗa da lambar yabo ta Nobel a shekarar 2008 akan ilimin sanin halittar ɗan adam da likitanci. Ya kuma jagoranci tawagar masana da suka gano ƙwayar cutar ƙanjamau (HIV) da kuma abun da ke jawo karyewar garkuwar jiki ( Aids) Rubutun da LifeSiteNews tayi, wanda aka buga ranar 19 ga Mayu, ya ambato wata hira da Montagnier wadda gidauniyar RAIR ta ƙasar Amurka suka fassara kuma suka wallafa a jiya. Gidauniyar ta bayyana kanta a matsayin wani yunƙuri don ƙwanto jamhuriyar mu daga mutane da ƙungiyoyin da suka haɗa kai don yaƙi da Amurka, tsarin mulki, iyakokin mu da kare ɗabi’un yahudu da nasara. A cewar LifeSiteNews , Montagnier ya kira allurar rigakafin cutar korona da abun da ba a yi tunani ba, kuma babban kuskure a tarihi da ke haifar da nau’ikan cutar, wadda ke ta jawo mace-mace daga cutar. Babban kuskure ne, ko ba haka ba? Kuskure a kimiyance, a kuma likitance. Kuskure ne da ba za a taɓa amincewa da shi ba, Sun wallafo Montagnier na cewa . Littattafan tarihi zasu tabbatar da haka, saboda allurar rigakafin ke jawo nau’oin cutar. Sai dai babu inda rubutun ya ambato Montagnier ya ce duk waɗanda aka yiwa allurar zasu mutu cikin shekaru biyu, ko kuma mu shirya ƙona gawawwaki. A ranar 27 ga Mayu, LifeSiteNews suka ƙara sabunta rubutun . Yayin da LifeSiteNews ta ruwaito abun da Montagnier ya faɗa, wasu masana kimiyya sun yi watsi da rubutun sa, na cewa alluran rigakafin na jawo sababbin nau’ikan cutar, sabon rubutu ya fara da cewa . Ya kuma ƙare da cewa : Abu na biyu shine, Montagnier bai ce duk wanda aka yiwa gwajin allurar rigakafin Covid-19 ‘zai mutu’ cikin shekaru biyu ba. Wannan maganar an ƙage ta, an danganta masa ita a matsayin labaran ƙarya da ya ke ta bazuwa. Ba mu samu wata hujja da ta tabbatar da cewa Montagnier yayi waɗannan kalamai ba. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url