PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-08-26 (xsd:date)
?:headline
  • Ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya Tinubu bai ce zai miƙa mulki ga ‘ɗan ƙabilar Igbo ba’ (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Wani saƙo a Facebook na iƙirarin cewa Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyyar All Progressive Congress(APC) a zaɓen Najeriya na shekarar 2023, ya ce zai miƙa mulki ga ɗan ƙabilar Igbo bayan ya gama wa’adin shekaru takwas yana shugabancin ƙasar. Zan miƙa mulki ga ɗan ƙabilar Igbo bayan na yi shekaru takwas ina mulki, saƙon ya ce Tinubu na cewa. Tinubu, wanda yayi gwamnan jihar Legas daga shekarar 1999 zuwa 2007, ya lashe zaɓen zama ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jami’iyyar APC. Shi zai riƙe tutar jami’iyyar a shekarar 2023. Ƙabilar Igbo na zaune ne a Kudancin Najeriya. Tun bayan dawowar demokaraɗiya a shekarar 1999, al’ummar Igbo basu riƙe shugabancin ƙasar nan ba . An rarraba saƙon sama da sau 800, sannan ya samu tsokaci har guda 12,000. Sannan an cigaba da yaɗa da’awar a wasu saƙonnin a wasu shafukan Facebook: a nan da nan . Tinubun ya ce zai miƙa mulki ga ƴan ƙabilar Igbo bayan yayi shugabancin ƙasa na shekaru takwas? ‘A’a, bai ce haka ba’ Saƙon bai bada cikakken bayani akan waje da lokacin da Tinubu yayi maganar ba. Binciken mu bai nuna mana inda aka wallafa maganar ba a sahihan gidajen jarida. Tunde Rahman, maitaimakawa Tinubu akan kafafen yaɗa labarai, ya shaidawa Africa Check cewa ɗan siyasar bai yi wannan maganar ba. A’a, bai ce haka ba, Rahman ya shaidawa Africa Check. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url