PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-08-26 (xsd:date)
?:headline
  • Tsohon shugaban ƙasar Najeriya Obasanjo bai buƙaci ƴan Najeriya da su samu bindigogi don kare kansu ba (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Zaɓen 2023: Kowa ya shirya, Fulani sun mamaye Najeriya. Sun gane yanzu cewa zasu faɗi akan Peter Obi, ku samo bindigogi babu mai kare ku- Obasanjo, saƙon na Facebook ya ke cewa tsohon shugaban ƙasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce. Fulani wata ƙabila ce da ke warwatse a wurare da dama na Africa. Su na nan da dama a Najeriya, Mali, Guinea, Senegal da Nijar. Obi ɗan siyasa ne a Najeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Labour Party . Obasanjo yayi shugabancin Najeriya daga shekarar 1999 zuwa 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar People's Democratic Party (PDP). Obi shine wanda ake ta yaɗa cewa shine a matsayin zaɓi na uku mafi ƙarfi bayan ƴan takarar shugaban ƙasa daga jam’iyya mai mulki ta All Progressive Congress party da jam’iyyar adawa ta PDP. Mafi akasarin Fulani Musulmi ne, kuma an san su da kiwon shanu da dabbobin gida. Sai dai, a cikin su akwai mayaƙan da ke da alhakin kai hare-hare akan al’ummomi a faɗin ƙasar. An sake yaɗa wata da’awar a kafafen sada zumunta cewa wasu Fulani na shirin karɓe Najeriya don mai da ita ƙasar Musulunchi . Arewacin Najeriya na cike da Musulmi yayin da Kiristoci da dama na zaune a Kudu. Wannan da’awar ta ranar 4 ga watan Yuli an sake maimaitata a wasu saƙonnin Facebook da Tiwita . Shin Obasanjo yayi wannan magana da zata iya tayar da hankalin ƙasa, ta zama barazana ga tsaro ? Tsohon shugaban ƙasar bai faɗi wani abu makamancin haka ba Ainihin saƙon bai bayyana cikakken waje da lokacin da Obasanjo yayi maganar ba. Babu kuma wani sahihin gidan jarida da ya ruwaito Obasanjon yayi maganar, ko maganar da ta danganci cewa ƴan Najeriya su ɗauki bindigogi. Irin wannan magana dole ace sahihan gidajen jarida sun ruwaito ta, kasancewar Obasanjo mutum ne da ake ganin girman sa a duniya, wanda kuma har yanzu ake damawa da shi a siyasar Najeriya. Yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa, Africa Check na ƙara cin karo da bayanai ko kalamai na ƙarya da ake danganta su ga ƴan siyasa. Wannan zai iya ɓata muhawarar siyasa a yanar gizo da kuma a zahiri, ya kuma ragewa masu zaɓe damar zaɓen waɗanda suke da cikakken bayani akan su. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url