?:reviewBody
|
-
Hoton ruwan ɗorawar fasta wadda ke da take kamar haka Coronavirus COVID-19 ALERT wato jan hankali akan Coronavirus Covid-19, fastar ta kuma jero cututtakan bayan anyi allurar rigakafin da ba’a cika samu ba, an rarraba hoton a ƙalla sau dubu a Facebook , har ma a Afrika ta Kudu. Jerin cututtakan sun fara da ciwon kai, wanda zai cigaba da tsananta har ya kai ga mutuwa farat ɗaya. Fastar na ɗauke da tambarin gwamnatin ƙasar Ireland , tana kuma cewa mutune su kai rahoton ciwon bayan anyi allurar rigakafin ga hukumar kula da ababen kiwon lafiya ta ƙasar wato HPRA. Tayi kama da irin fastocin da hukumar lafiya ta ƙasa wato Health Service Executive (HSE) ta ke rabawa mai bayani akan Covid . Amma ta gaskiya ce? Yanzu da ake da alluran rigakafin Covid da aka amince da su da dama, ko ɗaya daga ciki na jawo mutuwar farat ɗaya? Fastar na ɗaya daga cikin fastocin ƙarya Abubuwa da dama da basu dace ba sun bayyana cewa fastar ta ƙarya ce. Bata gama cike irin tsarin da HSE suke yiwa fastar su ba. Nasu na rubuta shawara ga kiwon lafiya wato Public Health Advice- ba jan hankali ALERT ba. Fastocin HSE na amfani da tambarin su ba tambarin gwamnatin ƙasar Ireland ba. Sannan kuma tambarin ma bai yi dai-dai dana gwamnatin ƙasar ba , an sauya shi inda ya ce jama’ar Ireland. Lokacin da kamfanin dillancin labarai na AP suka tantance fastar , mai magana da yawun HPRA ya ce, wannan ba abun da HPRA ta fitar ba ne ko wani saƙo daga hukumar lafiya ta Health Service Executive. Bolivia Verfica , wadda ke ƙasar Bolivia da ke Kudancin Amurka sun tantance fastar. Sannan kuma Journal , wani kamfani watsa labarai da ke Ireland sun taɓa tantance wata fastar ƙarya da ta kwafi irin tsarin HSE don yaɗa labaran ƙarya. Ko ciwo bayan anyi allurar rigakafin Covid-19 zai iya jawo mutuwar farat ɗaya? Alluran rigakafin basu da illa, suna hana kamuwa da Covid-19 Mahukunta a ƙasashe sun amince da amfani da jimlar alluran rigakafin Covid-19 guda 23 a faɗin duniya. Duk sun bi tsarin da ya dace don tabbatar da rashin illar su, da kuma ganin sun bada kariya daga cutar. (A duba kundun bayanai na Africa Check akan yadda ake amincewa da magunguna da alluran rigakafin a Afrika ta Kudu , Najeriya da Kenya .) Hanyoyin da aka bi sun haɗa da manyan gwaje-gwaje. Bayan an amince da alluran rigakafin, ana cigaba da bibiyar su don tabbatar da basu bayar da wata illa ba. Kuma cututtakan da ake iya samu bayan anyi kowacce allurar rigakafi daban ne.. Da dama daga cututtakan da ake iya yi bayan alluran rigakafin Covid-19 sun haɗa da zazzaɓi ko zogi ko kuma wajen da akayi allurar yayi ja, cewar Hukumar kula da cututtaka masu yaɗuwa ta Afrika ta Kudu (NICD). Sauran cututtakan sun haɗa da zazzaɓi mai zafi, kasala, ciwon kai, ciwon jiki, ƙuraje a wajen da akayi allurar, makyarkyata da gudawa mara yawa. Waɗannan cututtaka basa tsananta kuma basa wuce ƴan kwanaki. NICD ta bada gargaɗin cewa matsanantan cututtaka bayan anyi allurar - sun haɗa da rashin lafiyar da wani abu da jiki baya so ke haddasawa, wanda kuma kowacce irin allurar rigakafi zata iya jawowa- an taba kawo rahoton hakan. Amma wannan ba kasafai ya ke faruwa ba. A cikin wani ɗan littafi da babu kamar sa a shafin yanar gizo na HSE a Ireland, littafin ya ce: Kamar kowanne magani, alluran rigakafi na iya sa wani ciwo. Yawancin wannan na zuwa daga mai sauƙi zuwa matsakaita, na kuma gajeren lokaci, kuma ba kowa ne ke samun su ba. HSE - da kuma hukumomin lafiya a duk faɗin duniya - suna ba da shawarar cewa allurar rigakafi itace hanya mafi kyau ga jama’a don kare kansu daga Covid-19.
(id)
|