PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2022-10-27 (xsd:date)
?:headline
  • Ana maganin dafin saran maciji mai dafi da ɓawon bishiyar kashu? Ba’a yi, a nemi kulawar likita (so)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • A taƙaice: Wani saƙon Facebook da ke yawo a Najeriya na iƙirarin cewa za’a iya maganin saran maciji ta hanyar tauna ɓawon bishiyar kashu. Wannan dai ƙarya ce, wanda maciji ya sara ya yi gaggawar neman taimakon likita. A ƙalla mutane miliyan 2.7 macizai masu dafi ke sara a kowacce shekara. Tabbas 81,000 zuwa 138,000 daga ciki na rasa rayukansu, yayin da waɗanda suka rayu ke haɗuwa da wata naƙasa ta din-din-din . Yanki mai hamada na Afrika, yanki mai yawan ruwan sama na Asia, New Guinea, Tsakiya da Kudancin Amurka na daga cikin yankunan da suka fi gamuwa da saran macizai, inda aka fi sanin su da wuraren zafi masu fama da annobar- saran macizai . Wani saƙo da ke yawo a Facebook tun watan Satumba 2022, yayi iƙirarin cewa ɓawon bishiyar kashu na maganin saran maciji sosai. Saboda ruwan ɓawon na daidaita dafin saran macijin, saƙon ya ce. An maimata da’awar a nan , nan da nan . Wannan rubutu ya ambaci wani bincike da akayi a shekarar 2009 a matsayin madogara. Shin cin ɓawon bishiyar kashu zaiyi maganin dafin saran maciji? Mun bincika. Rigakafin dafi ce kawai maganin da aka sani da ke kiyaye mutuwa daga dafin saran maciji Binciken 2009 , sashen ilimin kimiyar halitta da ta sinadarai ta jami’ar Mysore da ke India ne suka gudanar da shi. A yayin binciken, anyi amfani da ɓerayen da aka saka musu dafin maciji mai dafi, sannan aka basu ruwan ɓawon kashu da aka haɗa a ɗakin gwaji . Binciken ya nuna cewa ruwan ɓawon ya hana zubar jini, kumburi da ciwo a wajen saran macijin. Hatsarin da ke tattare da dafin na nan, sai dai ɓerayen da aka sakawa ruwan ɓawon basu yi saurin mutuwa ba. Binciken ya tabbatar cewa ruwan ɓawon taimakon-farko ne mai taimakawa saran maciji mai dafi. Sai dai kuma, maganin da ya fi aiki da dacewa don gujewa mutuwa bayan saran maciji mai dafi shi ne amfani da maganin da aka daɗe ana amfani da shi kuma yake aiki wato rigakafin dafi . Bincike da dama akan zafin saran maciji sun tabbatar da wannan, har da ma binciken 2009 da aka kawo a wannan rubutu. Zafin saran maciji ciwo ne da dafin da ke cikin saran maciji mai dafi ke haddasawa. Rigakafin dafi magani ne da ke tsayar da tasirin dafin. Farfesa Nicholas Casewell , darakta a cibiyar bincike da kawo agaji akan saran maciji da ke Biritaniya ya shaidawa Africa Check cewa zafin saran maciji abu ne da ke buƙatar taimakon gaggawa. Ya bada shawarar a yi gaggawar kai waɗanda maciji ya sara wajen jami’an kula da lafiya don basu rigakafin dafi. Maganin saran macijin da kawai aka sani shi ne rigakafin dafi, ya ce. Wasu hanyoyin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta fitar akan kula da saran maciji , sun yi gargaɗi akan amfani da maganin gargajiya. Zasu iya jinkirta tasirin maganin asibiti, wanda hakan zai ƙara yin illa ba sauƙi ba. Ɓawon bishiyar kashu ba rigakafin dafi ba ne, kuma ba zai kiyaye mutuwa ko naƙasa daga dafin saran macizai ba. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url