PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-01-29 (xsd:date)
?:headline
  • Haɗin bekin soda da ruwan lemon tsami ba zai sa jiki ya zama mai sinadrin alkali (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Yadda zaka mai da jikin ka ya zama mai ɗauke da sinadarin alkalayin kamar da shi aka halicce ka- haɗin gida don samar da sinadarin asid, taken rubutun da aka raba a kafar sada zumunta ta Facebook a Najeriya a watan Junairun 2021. Rubutun yayi iƙi'rarin cewa haɗin bekin soda da ruwan lemon tsami zasu taimaka maka ka daidaita abun da ake cewa pH na jikin ɗan adam, ka kuma zamar da jikin ka mai ɗauke da sinadrin alkalayin. Rubutun ya ƙara da cewa wannan haɗi zai taimaka maka ka magance yawan asid a ciki ya kuma sauƙaƙa lalurar yawan asid a jiki. An rarraba rubutu a wani shafin Facebook da ya shahara , mai suna The Professor, wanda ya ke kiran kansa da gidan magungunan gargajiya da haɗin magunguna don waraka. Sun wallafa wasu ' magunguna' da ba'a tantance su ba . Akwai bayanan da ba'a tantance ba da dama na yawo a yanar gizo akan yadda za'a samar da asid ko samar da alkalayin a jiki da yadda za'a daidaita su. Kula da abun da za'a ci ba shi da tasiri wajen samar ko gyara abun da ake cewa pH a jini- aikin ƙoda da huhu ne yin hakan. Africa Check ta tantance da'awa makamanciyar wannan da ke cewa za'a iya cin ƙwayar cutar Covid-19 a abinci mai ɗauke da sinadarin alkalayin, wata da'awar kuma na cewa yawan sinadarin asid a jiki ne ke jawo cutar sankara . Shin akwai wata hujja a kimiyance da ta tabbatar haɗin bekin soda da ruwan lemon tsami na maganin yawan asid a jiki? Ku ziyarchi likita kawai A ƙaida ƙoda da huhu suna aikin daidaita yawan asid a jikin ɗan adam. Amma jiki kan zamo yana da yawan asid idan har ruwan jiki na da asid mai yawa . Abubuwa da dama ke haddasa hakan, akwai kuma maganin duk abun da ka sa sinadarin yayi yawa. Emmanuel Ekanem, ƙwararre likitan hanta da cututtukan da suka shafi ciki, kuma Farfesan lafiyar kananan yara a jami'ar Calabar ya shaidawa Africa Check cewa duk wanda ke zaton yana fama da wata cuta ya garzaya wajen masana kiwon lafiya don kulawar da ta dace. Jiki na daidaita yawan asid da kansa ta wata kafa da ke cikin jikin, a ce wani haɗi ne zai daidaita yawan asid ba daidai ba ne, likitan ya ce. Ekanem ya tabbatar da cewa jiki na daidaita abun da ake kira matakin pH a karan kansa ba tare da amfani da wani abu ba kamar yadda wannan rubutu na Facebook ya buƙata. Duk wanda yake zargin yana da wata cuta da zata sauya masu yanayin asid a jiki, likitoci zasu duba su bada taimakon da ya dace, likitan ya ƙara. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url