?:reviewBody
|
-
A TAƘAICE: Ba sai kun je da nisa ba a Facebook zaku ci karo da maganin ciwon sankara. Sai dai duk da cewa binciken ɗan itacen soursop da ke fitowa a wurare masu zafi, na nuna alamun nasara, amma babu binciken da ya isa a kira soursop da maganin sankara, haka nan an hukunta wasu mutanen da ke nuna cewa hakan ne. A watan Nuwamba 2022, wani guruf a Facebook mai sunan The Alkaline Momma suka buga wani bidiyo da yayi iƙirarin cewa soursop , wani ɗan itace da ke fitowa a wuri da ke da yanayin zafi, a kuma dazuzzukan wajen da ke yawan samun ruwan sama, wanda ke cikin rukunin ƴa’ƴan itacen fasadabur na iya magance cutar sankara. Taken da ke tare da bidiyon na tallata wani abu da aka yi da soursop mai tsada, wanda ake sayarwa a shafin kiwon lafiyar da ba ta asibiti ba. A ƙalla mutane 6000 suka kalli bidiyon. An yaɗa wasu saƙonnin da ke irin wannan iƙirarin a kafafen sada zumunta, galibi a sigar tallan abubuwan da ke ɗauke da soursop. Wani saƙon na Facebook ma cewa yayi ɗan itacen yafi maganin sankara na kemotarafi karfi sau 1000. Waɗannan da’awowi akan kiwon lafiya har sun sa wannan ɗan itacen samun guruf na kansa a Facebook, inda aka rarraba labaran yadda irin binciken da akayi don samun hujjar da ta tabbatar da da’awar da ake akansa akan lafiya. Waɗannan da’awowin sun samu bincike a kimiyance? Mun duba. Binciken na nuna alamun tabbata ... a kan ɓeraye da bututun yin gwaji Soursop, wanda ake kira da gabiyola, ana samun sa a dazuzzuka masu yawan samun ruwan sama na wurare masu zafi a faɗin Afrika, Kudu maso gabashin Asia da Amruka ta Kudu. A maganin gargajiya, wasu sassa na itacen, da suka haɗa da ɗan itacen, ana amfani da su don maganin cutuka da dama. Wannan amfanin da ake da itacen ya jawo bincike akan yiwuwar samun abun da zaiyi amfani ga lafiya daga ɗan itacen. Bincike da dama da akayi a akan abu mara rai , an duba tasirin ɗan itacen akan wasu tantanin halitta ko tsokar jiki, amma ba jikin ɗan adam ba. Ana kiran irin wannan bincike binciken bututun gwaji. Wasu binciken kuma sun binciki tasirin soursop a jikin ɓeraye da gafiyoyi. Wasu daga cikin waɗannan bincike sun nuna alamun tabbata. Binciken farko-farko sun nuna yiwuwar iya samun tasirin kiyaye kamuwa da cutar daga soursop akan sankarar ciki ta fankiriyas da ta mama . A kwanan nan , an bayyana yadda soursop ke rage yaɗuwar ƙwayoyin halittar cutar sankara. A shekarar 2021 nazarin sakamakon ɗinbim binciken da akayi sun tabbatar da cewa wasu abubuwan da ke jikin soursop zasu iya samar da abubuwan da zasu iya yin tasiri, da suka haɗa da ƙwayoyin halittar da zasu kiyaye tasirin cutar sankara. Amma dai kamar sauran binciken, waɗannan ma anyi su akan gafiyoyi, ɓeraye da wasu ƙwayoyin halittar jikin ɗan adam da aka keɓe. Masana ilimin kimiyya sau tari suna samun sakamako mabambanta , yayin da aka yi makamancin binciken akan ɗan adam, don haka ire-iren waɗannan bincike ana ganin su ne a matsayin binciken farko wanda bai kammala ba. Ba kasafai ake bincike akan ɗan adam ba. A wani bincik e an taɓa tambayar masu fama da sankarar mama ko suna shan soursop da wasu saiwowi. Binciken ya samu dangantaka tsakanin shan soursop da raguwar tsahon rayuwa bayan ƴan wasu shekaru. Amma ba ya nufin soursop ne ya jawo raguwar tsahon rayuwa ba. Sai dai mu ringa tunawa cewa haɗuwar bincike ba ya zama dalilin samuwar hujja. Gargaɗi da hukuntawa akan da’awowin ƙarya akan soursop Soursop bashi da wata illa wajen shan sa. Babu ma yiwuwar cewa don an sha abu mai ɗauke da girabiyola zai yi wata illa, a cewar wajen binciken sankara na UK . Amma likitoci sun yin gargaɗin shan zai iya jawo wata matsala ga wasu mutanen, kuma zai iya haɗuwa da magungunan hauwan jini da na wasu cututtukan. Saboda shaharar da yayi a matsayin magani ga mutane, sanannun cibiyoyin magunguna sun yi gargaɗi akan ɗan itacen. A shekarar 2017, hukumar kula da abinci da magunguna ta Amurka tayi gargaɗi ga kamfanoni 14 da ke iƙirarin ƙarya akan soursop da wasu hanyoyin maganin cutar sankara da ba na asibiti ba. Amintattun ƙungiyoyin cutar sankara sun musanta wannan da’awar, waɗanda suka haɗa da wajen binciken cutar sankara na UK , Cibiyar maganin cutar sankara ta Amurka da kuma ƙungiyar cutar sankara ta Afrika ta Kudu . Duk da cewa bincike akan gafiyoyi da cikin bututun bincike sun nuna alamun tabbatuwar da’awar, amma babu wata hujja da ta tabbatar soursop ko wani abu daga jikinsa na maganin cutar sankara a jikin mutane.
(id)
|