PropertyValue
?:author
?:datePublished
  • 2021-04-07 (xsd:date)
?:headline
  • Saiwar Afrikan baizil, jan dodon koɗi da ganyen lemongiras basa maganin basir (id)
?:inLanguage
?:itemReviewed
?:mentions
?:reviewBody
  • Maganin basir mai inganci (basir na ciki da na waje), ƙunshe a cikin wani saƙo da ke yawo a wani shafin Facebook Najeriya. Saƙon na iƙirarin cewa haɗa saiwar Afrikan baizil, jan dodon koɗi da ganyen lemongiras zai kawar da basir. Saƙon ya bayyana yadda za’a yi haɗin da yadda za’a sha, inda saƙon ke ƙarewa da: Ga basir na waje, a haɗa gari da man ja, sai a sa a dubura don rage raɗaɗin, sai a mayar da abun da ya fito. Fatan samun lafiya cikin gaggawa. Wannan haɗin da gaske zaiyi maganin basir? Mun bincika. Ana maganin sa da magunguna da kuma aiki Basir , na samuwa ne lokacin da jijiyoyin dubura ta ƙasa suka kumbura. Basir na ciki shine kumburin jijiyoyin dubura ta ciki, yayin da basir na wajen kumburin yana faruwa ne a ƙasan fatar dubura. Mun tuntubi Casimir Omuemu, Farfesan magunguna a jami’ar Benin da ke Kudancin Najeriya, ko wannan haɗi zai yi aiki. Sam baya aiki, ya ce. Wannan ba’a amince da shi ba, don magani a kimiyyance. Ya ƙara da cewa akwai hanyoyin maganin basir da suka haɗa da bada magani ko yin aiki. Ana bada magunguna don hana basir ɗin zubar jini, rage kumburi da kuma hana raɗaɗi. Mangunguna kawai basa maganin basir. Za’a iya yin aikin tiyata ko yin aikin zamani na endoscopy don magance basir ɗin. Ya yi bayanin cewa yayin endoscopy ana sa roba a ɗaure basir ɗin ko kuma ayi amfani da ɗumi a ƙone basir ɗin. Omuemu ya ƙara da cewa, duk lokacin da aka samu basir duk abun da akayi amfani wajen magani ba zai hana basir ɗin dawowa ba bayan wasu shekaru, musamman idan ba’a kula an kiyaye musabbabin basir ɗin ba, musamman matse bayan gida. Ya ce hanya mafi sauƙi ta kiyaye basir bata wuce kiyaye barin bayan gida yayi tauri, ta hanyar yawan cin kayan lambu da kuma shan ruwa da yawa. A kuma guji matse bayan gidan yayin da aka zo yin sa. Ya ƙara da cewa a kiyaye amfani da magungunan gargajiya don zasu iya jawo rauni, musamman waɗanda ake sawa a dubura. Adegboyega Fawole, Farfesa akan mata da kula da lalurar masu juna biyu a jami’ar Ilorin , Yammacin Najeriya,yace akwai yiwuwar mata zasu kamu da basir bayan haihuwa. An fi samun sa bayan haihuwa, saboda matsin ciki da kuma nishi yayin haihuwa, wannan ke raunana yanayin dubura. (id)
?:reviewRating
rdf:type
?:url